Kungiyar Kwallon Kafa ta Manchester United dake ƙasar Birtaniya ta sanar da cewa dubun-dubatan yan kallo ne sa su more cikin fili yayin karawarta ta karshe a gasar Europa League da Villareal.
A ranar Laraba ne 26 ga watan Mayun da muke ciki za a yi fafatawar ta karshe a birnin Gdanks na kassr Poland tsakanin Ƙungiyoyin biyu.
Gabannin zuwa zagayen karshen dai Manchester United ta wanke AS Roma ta kasar Italiya 8:5 gida da waje, yayin da Villareal ta kwaɗe Arsenal 2:1 gida da wajen.
Da ma dai a jiya Talata ne Manchester United ta yi wasan karshe a filin wasa na Old Trafford a wannan kaka inda ta yi gwajin yan kallo sama da 10, 000.
A yanzu haka kungiyar ta sanar da cewa za ta dukkanin yan kallo da suka saba shiga filin wasa su shiga larawar ta karshe ba tare da shamaki ba.