Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta bayyana aniyarta ta yin musanya da tsohon dan wasan ta Christiano Ronaldo da kuma dan wasan ta na yanzu Paul Pogba.
A yanzu haka idan wannan yarjejeniya ta tabbata, ta nuna cewa Ronaldo zai sake hadewa da tsohuwar zuma kenan tun bayan shekaru 12.
Jaridar La Gazzetta ta kasar Italiya ta ruwaito cewa kungiyoyin biyu sun kuduri aniyar dawo da tsofin yan wasan nasu a wani mataki na yaukaka dangantaka.
Yanzu haka United na bukatar kudi mai tsoka idan Juventus za ta dauki Pogba a hannunta, sai dai a bangaren Ronaldo ana ganin shi ma fa ka iya jan kilo.
Ronaldo mai shekara 36 ya lashe wa United kofunan Firimiya uku da kofun kalubale biyu da kofin zakarun turai daya gami da gasar FA, a tsawon shekaru shida da ya shafe a Ƙungiyar.
Ko da yake a tsagin Pogba shi ma ba kanwan lass ba ne domin ya lashe kofin duniya tsakanin 2012-2016 inda ya tande kofunan Serie A hudu da kuma kofin kalubale na kasar Italiya