Manchester United zata dauko Varane
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United na daf da dauko Raphael Varane dan wasan baya na Real Madrid. Kamar yadda Jaridar Espn ta wallafa.
Dan wasa Raphael Varane wanda kwantiragin sa zai kare a karshen kakar wasan 2022 a Real Madrid.
KARANTA:-Gwamnatin Nasarawa ta sallami fursinoni 36
Mai horas da kungiyar Manchester United ya nuna kudirin sa na dauko dan wasan zuwa Manchester United bayan kungiyar Real Madrid tace yana iya tafiya a duk lokacin da yaso.
Kungiyar Kwallon kafa ta Real Madrid tace ta yima dan wasan kudi miliyan 70 ga duk mai sha’awar daukan Dan wasan.
Inda kansu kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na yunkurin kawo sabbin Yan wasa don bunkasa aikin sabon mai horas da kungiyar Carlo Anceloti.