Manhajar e-Naira ta dawo a dandalin Play store bayan ta ɓace daga shafin tsawon awanni 24 da suka gabata.
Manhajar dai ta ɓace ne tun daga Jiya har kawo yau misalin ƙarfe 1:00 na rana, kuma kafin ɓacewar ta sama da mutane dubu 100 ne suka sauke manhajar.
Manhajar dai ta gamu da tazgaro ne bayan da dandazon jama’a ke ta kokarin shigar da Lambar BVN din su, hadi da adireshin su na Email.
Yanzu haka dai jama’a zasu iya komawa kan Play store domin sauke manhajar mai suna eNaira Speed Wallet.
Tuni dai wasu daga cikin yan Nigeria ke ci gaba da yada maganganu daban daban kan ɓacewar manhajar a Play Store.