By Ishaq Dabai
Bayan shafe kusan wata guda a tsare Manjo Christopher Datong, wanda ‘yan bindiga suka sace daga gidansa a Kwalejin Tsaron Najeriya NDA da ke Kaduna, a ranar 24 ga Agusta 2021, ya shaki iskar ‘yanci.
‘Yan bindigar sun kai hari tare dayi garkuwa da Datong a babban sansanin sojoji da ke Afaka, Kaduna, bayan da suka kashe jami’anta biyu da aka bayyana sunayensu Laftanar Wulah da Flight Lieutenant Okoronkwo.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN, yace nakalto Ezindu Idimah wani Kanal kuma Mataimakin Darakta, hulda da jama’a na runduna ta daya a Kaduna, wanda ya bayyana hakan, a cikin wata sanarwa cewa an kubutar da jami’in a ranar Juma’a, ya kara da cewa an lalata sansanin ‘yan ta’adda da yawa a yankin Afaka- Birnin Gwari yayin da aka kashe’ yan ta’adda da yawa yayin aikin ceton.
Bayan isa sansanin, sanarwar ta ce, ana zargin wurin da ake tsare da Datong, sojojin sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar kuma ana cikin haka ne aka ceto jami’in da aka sace, inda ya kara da cewa jami’in ya samu rauni kadan, amma An yi jinyarsa a wani asibiti kuma an mika shi ga NDA don ci gaba da aiki.
Idimah ya ce “Ayyukanmu za su ci gaba har sai mun kamo ko kuma mu kawar da maharan da suka kashe jami’ai biyu a cikin NDA a ranar 24 ga Agusta 2021,” in ji Idimah.
Comments 1