Gwamna jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce Akalla ’yan asalin jihar 16,000 ne za su ci gajiyar shirye-shiryen tallafin noma da aka kaddamar jiya Alhamis a jihar.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirye-shiryen, gwamnan ya bayyana shirin a matsayin wani babban ci gaba ga shirin gwamnatinsa na noma, da nufin samar da ayyukan yi da samar da abinci ga al’ummar jihar.
Gwamnan ya kara da cewa shirye-shiryen na da nufin inganta rayuwar manoma musamman mata da masu bukata ta musamman da kuma karfafa gwiwar ‘yan asalin jihar da su shiga noma domin dakile matsalar karancin abinci da ke kunno kai a kasa.
Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da kulla kwakkwarar hadin gwiwa tare da abokanan ci gaba domin bunkasa noma a jihar.
Shirye-shiryen hadin gwiwa ne hukumar KNARDA, kungiyar bunkasa noma da makiyaya ta jihar Kano (KSADP), SASAKAWA, APPEALS da kuma shirin NG-CARES.