A yayin da Nigeria ke bikin cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai, a jihar Taraba wani abun ban tausayi ne ya faru.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa an gano gawarwakin manoma 15 a wani hatsarin kwale-kwale a kauyen Gwamtamu da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba.
Rahotanni sun bayyana cewa, lamarin ya faru ne a lokacin da manoman ke kokarin girbe amfanin gonakin da suka noma a wani filin noma da ya mamaye.
KARANTA ANAN: Zamu Cigaba Da Tallafawa Hukumomin Tsaron Jihar Yobe – Inji Gwamna Buni
Manoman da yawansu ya haura 50, an ce suna cikin kwale-kwale 12 suna yin sintiri domin girbin masara a lokacin da kwalekwalen ya kife sakamakon ruwan sama da iska mai karfi.
“Akwai kimanin manoma 50 a cikin kwalekwalen kuma yawancinsu sun fado daga kwalekwalen da ke cikin ruwa. Kuma zuwa ranar Asabar, gawarwakin mutane 15 ne kawai aka gano yayin da wasu da dama suka bace,” inji wata majiya.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, an tattara tawagar masu bincike zuwa wurin, kuma a halin yanzu suna kokarin zakulo wasu gawarwaki.
Da aka tuntubi jami’in yada labaran jihar DSP Usman Abdullahi, ya ce har yanzu ba a yi wa rundunar ‘yan sandan jihar bayani kan lamarin ba.
Sai dai ya ce da zarar rundunar ta samu cikakken bayani game da lamarin, zai yi karin haske.
A wani labarin kuma: Indonesian: Mutum 174 Sun Mutu, Yayin Turmutsutsu A Filin Kallon Kwallon Kafa
Akalla mutane 174 ne suka mutu sakamakon turmutsitsin da ya barke a wasan kwallon kafa a Indonesia tsakanin Arema FC da Persebaya Surabaya, bayan da ‘yan sanda suka harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa fusatattun magoya bayan kungiyoyin kwallom daga filin wasan.
Lamarin ya faru ne a daren ranar Asabar a Malang, inda magoya bayan kungiyar Arema, suka mamaye filin wasa bayan da kungiyar ta sha kashi na farko a gida a hannun Persebaya Surabaya cikin shekaru 23.