Manoma a wasu Al’ummomi a Sokoto suna kokawa, biyo bayan gagarumar asara a dalilin canjin yanayi, musanman iska wanda ya lalata amfanin noman su.
Ɗaya daga cikin manyan sana’o’in, da abinci ga Al’ummar Sokoto shine noma, amma yana fama da gagarumar matsala a dalilin iska da canjin yanayi ya janyo, da kuma wasu matsaloli da suka haifar ga amfanin gona.
Wakilin Majiyar mu ya shaida cewa iska mai ƙarfi ya lalata amfani a gonaki, musamman shinkafa, Masara, da gero, kuma sun samu matsalar ne a lokacin da suka je girbi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Cin Hanci ‘Cancer’ ce, dole mu magance ta — Osinbajo
A tattaunawa da wakilin Majiyar mu da wani Manomi Muhammadu Auwal da Bello Umar ya bayyana irin yanayin daya tsinci kanshi na rashin jindaɗi inda yace lamarin ya shafi gonakin sa da abinci,a yayinda yunwa ta fara yawaita saboda ƙarancin Abinci.
A lokacin da wakilin Majiyar mu ya ziyarci gonar sa dake Gidan Ariju a Ƙaramar Hukumar Kware ta Jahar Sokoto Arewa maso Yamma, Muhammadu Auwal mai shekaru 38 da ɗiyansa guda 3, sun samu shinkafa marar yawa saboda matsalar data afku.
A cewar sa, ya kan noma shinkafa, gero, da Masara kuma yana samun amfanin gona mai yawa, amma iska mai ƙarfi ya lalata amfanin gonar sa, wanda yayi sanadiyar faɗawar sa da iyalan sa cikin talauci.
A cewar Gwamnatin Jihar Sokoto, ta hanyar Kwamishinan Noma Farfesa Aminu Abubakar, ya bayyana cewar gwamnati zata taimaki manoman domin ƙarfafa masu gwiwa akan aikace-aikacen su na Noma a Jahar.