• Gwamnatin tarayya ta mika aikin Madatsar Ruwa na noman Rani ga manoman Jigawa da kudin shi ya kai naira billiyan 10.
• Ministan Albarkatun ruwa na Kasa ne ya mika aikin ga Gwamnan jihar Jigawa, inda ya ce Nan da shekarar me zuwa aikin zai kammala dari bisa dari.
• Abashi jawabin gwamnan Abubakar Badaru ya yaba wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa irin kokarin da ya ke yi.
A jiya Asabar Gwamnatin tarayya ta mika aikin madatsar ruwa na noma rani, da kudin shi ya kai naira billiyan goma, ga Manoma mabukata dake Karamar hukumar Auyi na jihar Jigawa.
Ai kin gonan wanda ya kai sama da hekta dubu biyu, ya sami tallafi ne daga bankin Duniya, domin tallafa wa manoman karkara da nufin yin aikin gona, rani da damina.
Hukumar dake kula da bunkasa rafin Hadejia da Jamaare HJRBDA ce ta jagoranci gabatar da wannan gagarumin aikin.
Lokacin da ya ke mika ragamar aikin ga Gwamna Badaru Abubakar na jihar Jigawa a kauyen Yamdi, Ministan albarkatun ruwa na Kasa Suleiman Adamu , ya bayyana aikin amastayin cika alkawarin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa al’umar yankin, lokacin da ya ziyar ce su a tun shekarar 2018.
KARANTA WANNAN LABARIN: Daso ta yi kira ga yammata Yan fim da su kare mutuncin su
A cewar Ministan akalla Manoma mabukata sama da dari biyu ne za su amfana da wannan aikin da aka mika a jiya Asabar.
Ya kara da cewa, yanzu haka ankammala kashi 74 cikin dari na aikin, Wanda nan da watan Yunin shekarar Mai zuwa, aikin zai kammala dari bisa dari.
A na shi sakon, Gwamna Badaru, ya yaba wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa irin kokarin da ya ke yi, inda ya kara da cewa, mika madatsar ruwan zai taimaka wa wadanda za su amfana rage kashe kudaden su, wajan siyan kayan aikin nomar rani.
Comments 2