A ranar Juma’a ne 16 ga watan Yulin 2021 manyan Antoni Janar na kasarnan shiyar kudu maso yammaci, suka yi wata ganawar sirri a birnin Ado-Ekiti fadar gwamnatin jihar Ekiti.
Abubuwan da aka tattauna a taron sun hada da sanya hannu kan kudirin baiwa ɓangaren Shari’a na jihohi ƴancin gashin kansu da kuma Majalisar Jihohi da dai sauran muhimman batutuwa.
Kazalika sun tattauna batun gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin shekara ta 1999 gami da gama bangaren shari’ar yankin kudu maso yammacin kasar ya zamto na bai-daya.
Kawo yanzu dai da muke hada muku wannan rahoto, Manyan Antoni Janar din ba su fitar da sakamakon wannan tattaunawa ba.
To sai dai kamar yadda aka sani wannan ba shine karon farko da ake samun irin wadannan tattaunawa ba a faɗin kasar, lamarin dake zama tamkar an shuka wato shiru kake ji.