Ƙasar Rasha ta yi nasara kaddamar da har ba Tauraron ɗan adam na kasar Iran zuwa sararin samaniya duk kuwa da damuwar da Amurka ta nuna kan buƙatar yin hakan.
An kaddamar da Tauraron Ɗan adam din ne mai suna Khayyam a Baikonur da ke cikin Kazakhstan.
A makon da ya gabata Manyan Jami’an Amurka sun bayyana wa Jaridar Washington post cewa suna fargabar kada Rasha ta yi amfani da Tauraron wurin leken assirin sojojin Ukraine, amma kuma Iran tace za a yi amfani da shune wurin kula da muhallin kasar kuma gwamnatin Iran ce zata kula dashi.
Rasha ta dai dade tana kokarin neman nasara a yaƙin da ta keyi a Ukraine yayin da mahukunta suke zargi Hukumar kula da yanayin Rasha da faɗa wa Gwamamnatin Iran cewa su zasu kula da Tauraron ɗan adam tsawon watanni domin taimakamata a yaƙin da ta keyi.
CG Ya Shawarci ‘Yan Kasuwar Katako Da Su Samar Da Wuraren Kashe Gobara
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito wata majiya da ta bukaci a sakaye sunan ta, ta bayyana cewa, tauraron dan Adam din, yana iya baiwa ƙasar Iran da Rasha damar amfani da Tauraron domin kula da ayyukan soji da wurin da sojojin kasashen ke zaune.
Sai dai wata sanar wa da Iran ta fitar, ta karyata wasu hotuna da aka yada dake nuna amfani da tauraron wurin ayyukan soji.
Gwammanatin iran tace tuni Hukumar kula da sararin samaniyar ƙasar ta karbi bayanai farko akan tauraron dan Adam din.
Harba tauraron dan Adam din ya zo ne makonni uku bayan da shugaba Vladimir Putin ya ziyarci shugaban addinin kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei a birnin Tehran.
Haka kuma, Lamarin yazo dai dai da lokacin da ake kara samun zaman dar-dar tsakanin Amurka da Iran, bayan da kungiyar tarayyar Turai ta bayar da bayanenta na karshe da ke neman sake sabunta yarjejeniyar Nukiliyar Iran.
A yanzu dai zabi ya ragema manyan jami’an gwamnati Amurka na su sanya hannu ga bayanan da aka gabatar musu na yarjejeniyar ko kuma su yi buris da shi.
Shi dai tauraron dan adam din na Khayyam an rada masa suna ne domin tunawa da fitaccen marubucin nan kuma masanin tsarin rayuwar dan adam na yankin Pasha Omar Khayyam.