Daga: Muhammad Gambo Damaturu
Gwamnatin jihar Yobe ta ce babu wani bashi da manayan likitocin da suke duba marasa lafiya a jihar da suke binta na alawus.
Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Muhammad Lawan Gana ne ya bayyana haka ranar Larabar nan a wani taron manema labarai.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Kwamishinan ya ce “Manyan Likitoci dake zuwa duba majinyata a asibitocin Jihar Yobe basu taba bin Jihar bashin alawus ba”.
KARANTA KUMA: Likitoci Masu Neman Kwarewa Sun Tsawaita Yajin Aikin Su
Lawan Gana ya bayyana irin nasarorin da suka samu cikin shekaru ukun da suka gabata, inda yace bangaren kiwon lafiya na daya daga cikin fannoni hudu da wannan Gwamnatin tafi baiwa fifiko.
Yace a cikin shekaru ukun da wannan Gwamnati tayi, ma’aikatar kiwon lafiya ta samu nasarar gina cibiyar jinyar mata da yara kanana mai gadaje 200, dakin kebe masu jinya, ginawa tare da kwaskwarima ga cibiyoyin kiwon lafiya guda 138 daga cikin guda 178 da ake da niyyan samarwa a mazabun jihar.
Ya kara da cewa gina dakin ajiyar magani da kuma daukar kwararrun jami’an kiwon lafiya da sauransu, duk wannan gwamnati ta mu tayi domin amfanar al’ummar jihar nan.
Ya kuma bayyana cewa zancen da ake yadawa cewa Gwamnatin Jihar Yobe bata biyan Likitoci masu zuwa duba majinyata daga wurare daban-daban ba wannan batu ba gaskiya bane, bashi da tushe balle makama.
“Babu Likitan da yake bin Gwamnatin nan bashi na alawus dinsa kamar yadda ake yadawa“, inji Kwamishinan.
Tun farko a jawabin maraba, Shugaban Kungiyar ‘Yan Jaridu reshen Jihar Yobe, kwamaret Rajab Muhammad ya godewa Kwamishinan da sauran shuwabannin hukumomin dake karkashin Ma’aikatar lafiya kan amsa gayyatan da sukayi.
A wani labarin kuma: Atiku Ya Kai Ziyara Enugu, Da Reechoes Yayi Alkawarin Sake Gina Najeriya
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar a ranar Talatar nan ya ziyarci jihar Enugu inda ya sake jaddada alkawarin sake gina kasar.
Atiku, wanda tsohon mataimakin shugaban kasa ne, ya samu rakiyar mataimakinsa Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta a ziyarar ga masu ruwa da tsakin jihar.