Shugaban darikar Tijjaniyya na kasar Aljeriya, Sheikh Aliyu Bil Arabi da sauran manyan malaman darikar na birnin Kano domin gudanar da addu’ar domin samun zaman lafiya da cikakken tsaro a fadi kasa Najeriya.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya fara tarbar Sheikh Aliyu Bil Arabi tare da tawagarsa a gidan gwamnati dake Kano, kafin daga bisani su wuce filin wasa na Sani Abacha dake kofar Mata a Kano.
Daga bisani an tarbi Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.
Gwamnatin tarayya ta samu wakilcin karamin ministan noma na kasa Mustapha Baba Shehuri a wajen taron.
Mabiya Darikar Qadriyya da sauran su, na daga cikin wadanda suka halarci taron yi wa kasa addu’ar