Manyan Motoci biyar da kanana biyu sun kama da wuta a Ogere
Kawo yanzu dai manyan Motoci guda hudu sun kone kurmus akan hanyar Ibadan zuwa Legas.
Wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin yace Motoci biyar manya da kanana biyu sun kone Wanda aka tabbatar da mutane biyu suka mutu.
KARANTA:- Nasarorin Sanata Uba Sani cikin shekara biyu.
Kamar yadda Jaridar Tvcnews suka ruwaito wata babbar mota mai dauke da kayan abinci ta fadi a babban hanyar inda ta rufe hanyar gaba daya sai ga wata mota mai dauke da fetur ta gabza mata nan take ta kama da wuta ya jazama sauran Motoci bakwai dake kewayansu.
Babatunde A. Ya bayyana cewa gan-gamin mutane wadanda suka hada da FRCN, NPF da sauran Mutanen gari suka hadu wajan dakatar da wutar.
Ya shawarci masu Motoci dasu canza hanyar har sai lamarin yayi sauki.
Comments 1