Hukumar kididdiga ta Nijeriya, NBS ta tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya marasa aikin yi sun kai miliyan ashirin da daya, da dubu dari bakwai da dari shida da sha bakwai (21,764,617).
Wannan kididdigar yana cikin rahoton da hukumar ta wallafa a shafinta na Intanet wanda ta yiwa take da “Rashin aikin yi da rashin cikakken aiki ”, wato “Unemployment and Underemployment Report (Q2 2020)”.
Sun bayyana rahoton a matsayin binciken da suka yi a lokacin cutar korona zuwa watan Agustan 2020. Sun tabbatar da cewa rashin aikin yi din a yayin wannan annobar cutar ya tashi da kashi 23.1 a karshen watannin shekarar 2018 zuwa kashi 27.1.
Sun kara da cewa karuwar marasa aikin da aka samu yana nuna cewa masu neman aikin yi sun karu ne, wanda suka ce hakan na nuna cewa wadanda suke ayyukansu na kwadago sun dawo suna neman aikin yi ke nan. “ko kuma wadanda suke ayyukan su a baya, sun rasa aikin, inda a yanzu suke neman wasu ayyukan. Ko kuma duka abu biyun ne ya auku.” Rahoton ya tabbatar.
Jaridar Madubi ta labarto cewa, rahoton ya tabbatar da cewa; wadanda suke da ayyukan yi a daidai wannan lokacin sun kai mutum miliyan hamsin da takwas, da dari biyar da ashirin da bakwai da kuma dari biyu da saba’in da shida (58,527,276).
Wanda kididdiga ke nuna cewa masu ayyukan yi din ba su wuce kashi 15.8 ba a watanni ukun 2020.
Rahoton ya ce cikin wadancan adadin, mutum 35,585,274 kawai suke aiki na dindindin, inda suke ayyukan awa arba’in cikin kowanne mako. A yayin da mutum 22,942,003 suke aikin wucin gadi na tsawon awa 20 zuwa 29 a duk mako.