Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjina wa tsohon shugaban kasar marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua bisa kishin talakawa da ya nuna lokacin yana raye.
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Malam Garba Shehu ya fitar ranar Talata ta ambato Shugaba Buhari yana cewa duk da bambacin siyasar da ke tsakaninsu, amma ya tabbatar marigayin mutum ne mai kishin ƙasa.
“Duk da bambancin siyasar da ke tsakaninmu, tabbas Shugaba Yar’Adua mutum ne mai kishin saboda shauƙinsa a kan talakawa da kuma soke tsare-tsaren da ya yi amanna an yi su ne domin gallaza wa ‘yan Najeriya marasa ƙarfi, a cewar Shugaba Buhari.
Ya kara da cewa: “Ya kamata a jinjina wa dukkan shugaba kan ayyukan alheri da ya yi, ko da kuwa ka yarda da ra’ayin Shugaba Yar’Adua na siyasa ko baka yarda da shi ba, kuma zan iya cewa dole tarihi ya tuna gaskiyarsa da jajircewa wurin yi wa ƙasa hidima.
Ranar Talata marigayi Yar’adua ya cika shekara goma da rasuwa.
Ya mutu ne ranar 5 ga watan Mayu na shekarar 2010 bayan ya sha fama da rashin lafiya lokacin yana kan mulki.
-Bbc Hausa