Daga Muhammad Garba
Na karanta tare da ra’ayoyi daban-daban na wata kasida mai taken: “Gargadi ga Gwamna Ganduje da masu tunani irin nasa” wanda Femi Fani-Kayode, tsohon ministan Tarayyar Najeriya ya rubuta.
Idan aka shiga cikin abubuwan da labarin ya ƙunsa mutum zai iya fahimtar cewa marubucin ko dai ya jahilce Gwamna ko kuma anyi masa bayani ba daidai ba.
Wannan wani yanki ne na rubutun da ke cike da kalamun batanci wanda ya nuna abinda aka faɗa ba gaskiya ba ne a kan wani bayani da aka ce Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya yi wanda a ciki aka ce Gwamna ya zargi Igbo da Yarabawa da neman ƴanci, wai “Ta haka ne suke haifar da rashin tsaro tare da kafa IPOB da Oduduwa Republic wadanda yanzu ke addabar dukkan al’ummar kasar.”
Wanda aka yi ta ɗauka a na zagayawa da shi a yanar gizo, abin takaici ma shine, yadda ba za a iya kafa hujjar ko yaushe ne gwamnan yayi wannan bayanin ba. Kuma marubucin ya kasa faɗin haka. Abin mamaki, mun yi tsammanin Fani-Kayode a matsayin lauya ya kamata ne ya zama mai nuna damuwa game da sakamakon yin irin wannan zargin, musamman ma inda yake amfani da kalmomi ga Gwamna.
Ba nufina ba ne in hada kai da shi ko kuma mayar masa da martani bisa son zuciyarsa, ganin cewa masu hankali za su san gaskiyar lamarin a koyaushe, na yi mamakin takamaiman abin da Fani-Kayode zai iya samu ta hanyar yin irin wannan zargi a kan gwamna.
Babu yadda za ayi Ganduje ya yi wannan maganar. domin Ya kasance ɗan Nijeriya mai Bin doka da Oda wanda ke da abokai da yawa a duk faɗin ƙasar, a cikin Igbo da Yoroba, Yana rike da sarautar Agu Na Eche Mba ta kasar Igbo wacce majalisar sarakunan gargajiya ta kudu maso gabas suka bashi.
Yana cikin tsofaffin ɗalibai na Jami’ar Ibadan, kuma ba da daɗewa ba aka sanya shi cikin jerin tsaffin ɗalibai 11 da suka fi Daraja da kima A Jami’ar, kamar yadda Farfesa Elsie Adewoye ta gabatar.
Har ila yau, Ganduje dan kishin kasa ne idan aka yi la’akari da salon shugabancinsa wajen tafiyar da al’ummomin kabilu daban daban tare da nuna kauna da kishin kasa. Tun lokacin da ya hau mulki a shekarar 2015, kabilun da ke Kano suka samu kusanci da gwamnatinsa fiye da duk wata gwamnati a tarihin Kano.
Baya ga shirye-shiryen ci gaban da ba a taba yi ba sai a gwamnatinsa wadanda suka shafi yankin Sabon Gari da ke karamar hukumar Fagge, wadanda galibinsu ke dauke da kabilu da ba ‘yan asalin jihar ba ta hanyar gina hanyoyi da gyara su, Ganduje shi ne kadai Babban Shugaba da ke daukar kwararan matakai don shawo kan matsalar tsaro wajen sanya doka da oda a yayin rikicin kabilanci a wani sashin kasar, ta hanyar kiyaye lafiya rayukansu da dukiyoyinsu.
Gwamna ya tabbatar da cewa duk wanda ya zaɓi ya zauna a Kano ba za a taɓa masa magana cewa ba ɗan ƙasa ba ne shi. Kuma na San abinda ya faɗa gaskiya ne, ya nada manyan hadiman cikin gwamnati daga manyan kabilun da ke zaune a Kano. A hakikanin lokacin da aka gabatar da sanarwar ficewa daga kungiyar hadin kan Matasan Arewa, dole ne a matsayin sa na Gwamna ya sanya baki ta hanyar kiran wasu tarurruka a Fadar Gwamnatin Kano, ba wai kawai don magance tashin hankalin ba, har ma da ƙoƙarin daidaita rikicin.
Haka kuma gwamnatin ta Ganduje ta gabatar da taron shekara-shekara na addinai da al’ummomi don karfafa imani da dankon zumunci tsakanin al’uma, zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a jihar Kano.
Duk da cewa Gwamna bafulatani ne, amma hakan bai hana Ganduje ya bayar da ɗiyar sa Fatima, ga Idris Ajimobi, Ɗan tsohon gwamnan jihar Oyo ba.
A matsayinsa na minista na lokaci daya, Fani-Kayode ya kamata ya himmatu wajen yada kyawawan manufofi don hadin kai da ci gaban kasarmu ba tunanin wasu abubuwa ba. kamata ya yi ya koyi ɗabi’u mafi kyau fiye da wulakanta wata ƙabila ko shugabancinta.
Lokaci ya yi da Femi Fani-Kayode zai koyi girmama kansa ta hanyar daina yin maganganun da ba su da hujja tare da kalaman ɓatanci ko ƙiyayya ga wasu ƙabila.
Mohammed Garba shi ne kwamishinan yaɗa labarai, na jihar Kano.