Ƙungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya IPMAN reshen jihar Kano ta sanar da gwamnati kan wani shiri da wasu masu zaman kansu ke yi na kara farashin man fetur a kasar.
Shugaban kungiyar IPMAN reshen jihar Kano, Alhaji Bashir Danmallam ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar kwanan baya a Kano, inda ya ce matakin zai haifar da rikicin mai a kasar.
Al’umma da dama dai na ta yin Allah wadai da wannan matsalar ta rashin mai, wadda suke tsammanin masu gidan man suna rufe gidan man ne ba don babu man ba.
Yanzu dai kusan gidajen mai Dari ne suka kulle a jihar Kano, yayin da kadan suka budewa shi kuma yake kasancewa cike da jama’a.
Al’umma dai na fatan ganin gwamnati ta shiga tsakanin domin samar musu da maslaha a tsakanin su.
Comments 1