Jam’iyyar APC reshen jihar Kano ta zargi jamiyyar NNPP, da gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf da aiwatar da ayyukan don zuciya, ta hanyar fakewa da rushe gine ginen jama’a.
Mataimakin shugaban jam’iyyar na Kano Hon Shehu Maigari ne ya yi Allah wadai da aikin jam’iyyar ta NNPP, a yan kwanaki da kama mulkin jihar.
KU KARANTA: Gwamnatin Kano Ta Kori Jami’an Dake Kula Da Cibiyoyi Hajji, Ta Rusa Otal
Maigari yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a satakariyar yan jaridu ta Kano, ya ce jamiyyar ta sanya da yawa daga cikin matasan jihar sun koma barayi, Maimaikon mutane na gari.
A cewarsa, jihar Kano babban gari ne da ya yi suna wajen kasuwanci, ba a Najeriya kadai ba, hatta a nahiyar Africa baki daya, amma abun takaici shine yadda jam’iyyar NNPP ke neman rusa wancan kambu na jihar.
Dangane da yadda al’umma ke ci gaba da asarar dukiya, sakamakon ayyukan don rai da gwamnan na Kano ke aikawarwa, APC ta bukaci daukacin al’umma su dukufa addu’a domin samu saukin asarar da gwamnan jihar Abba Gida Gida ke yi.
Daga nan kuma sai jam’iyyar ta bukaci wadanda lamarin ta shafa, akan su kara kwantar da hankali tare da mayar da komai ga, da kuma bin dukkan hanyoyin da suka kamata wajen Kalubalantar ayyukan Gwamnan a Kotu.
A wani Labarin kuma: Majalisar Wakilai Ta Caccaki Jirgin Nigeria Air Da Aka Kaddamar
Majalisar wakilai ta Kasa ta caccaki jirgin Nijeriya Air wanda aka kaddamar a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Majalisar ta bayyana kaddamar da jirgin na Najeriya a matsayin damfara.
Shugaban kwamitin majalisar kan harkokin sufurun jiragen sama, Nnolim Nnaji ya bayyana kaddamar da kamfanin na Nigeria Aor a matsayin yaudara bayan da manyan masu ruwa da tsaki a yarjajeniyar da aka yi tsakanin gwamnatin tarayya da kamfanin jiragen saman na Habasha suka musanta labarin kaddamar da jirgin.