Fadar Shugaban kasa ta ce babu wani cikin tubabban ‘yan Boko Haram 601 da za a dauka a aikin soja, sabanin yadda wasu suke yadawa.
Babban mai taimakawa Shugaban kasa kan harkokin watsa labarai, Malam Garba Shehu, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a Abuja ranar Laraba.
Hadimin na shugaban kasa ya kara da cewa babu wani daga cikin tubabbun da aka taba dauka a aikin soja, inda ya ce gwamnati ma bata taba shawarar yin hakan ba.