Kungiyar Kula da Sharar Jama’a ta Kano (KIWMA), ta gudanar da taron wayar da kan jama’a kan yadda ake sarrafa sharar a jihar.
Shugaban kungiyar, Dakta Bala Muhammad Tukur, ya ce an shirya taron wayar da kan jama’a kan kalubale da illolin zubar da shara da kuma samar da mafita kan yadda za a shawo kan matsalar.
“Mun gayyaci jama’a daga jami’o’i da sauran masana da masu ruwa da tsaki don tattaunawa, wayar da kan jama’a kan bukatar da ta dace wajen sarrafa shara. Babban taron bitar shi ne a gayyaci kowa da kowa don sanya hannu a kan lamarin, domin ganin mun magance kalubalen,” inji shi.
Yas bayyana cewa a matsayinsu na masu samar da ayyuka a yankin, KIWMA tare da hadin guiwar kamfanoni ne da ke gudanar da ayyukan sarrafa shara a jihar suka shirya Taron, ya kara da cewa ya zama wajibi su hada kai domin gwamnati ba za ta iya ita kadai ba.
Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Kano, Alhaji Kabiru Ahmed Getso, wanda Daraktan ayyuka na ma’aikatar Malam Sha’ayau Abdulkadir Jibrin ya wakilta, ya ce kwarin gwiwar matakin da kungiyar ta dauka ya dace, kuma a matsayinsu na masu mulki za su taimaka wa kungiyar. domin cimma manufofinta da kuma amfanin jihar.