Wadansu masana tattalin arziki sun nuna damuwarsa dangane da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na yin lissafin kasafin kudin 2020 bisa la’akarin da karin haraji da ta yi na kashi 7.5 sabanin kashi 5 da ake karba.
Idan ba ku manta ba, Kwamitin zartarwa na gwamnatin tarayya tuni suka amince da karin haraji kayayyaki daga kashi 5 zuwa 7.5. Inda wadansu ke ganin cewa hakan zai haifarwa da matsaloli musamman ga Talakawa.
Dr Patricia Auta, wani masanin tattalin arziki a yayin da yake maida martani ga kasafin kudin 2020 na naira tiriliyan 10.33 wanda shugaban kasa ya mikawa majalisar kasa a ranar Talata a Abuja, ya ce gwamnatin ba ta nuna kwarewa ba da ta yi amfani da batun karbar haraji da kashi 7.5 a maimaikon kashi 5 wajen rubuta kasafin kudin.
Auta ya ce ya kamata a ce batun karin harajin har sai majalisar kasa ta amince da shi kafin a kai ga amfani da shi.