Fitaccen jarumi a masana’antar finafinan Hausa ta Kannywood wanda ya dade ana damawa da shi, ya bayyana masana’antar da cewa a yanzu babu tarbiyya a cikin ta.
Jarumi Fagge ya bayyana hakan, ne a lokacin wata hira ta musamman da jaridar Dimokuradiyya ta yi da shi.
A tattaunawar an mayar da hankali ne game da halin da masana’antar ta samu kanta a ciki a wannan lokaci.
KARANTA ANAN: Ma’aikatan Jiragen Sama Sun Tsayar Da Aiki A Filin Jirgin Saman Kano
Tahir Fagge ya ce “A lokacin baya da muke jagorancin masana’antar mun samar da tsari sosai, kuma wadanda suka taso a cikin mu suke yin harkar a yanzu za ka ga suna da wannan tarbiyyar.
Don haka a yanzu kawai dai abin da nake gani a masana’antar, tarbiyya ce babu, don haka idan ka yi magana sai a ce kai ba gwamnati bane, amma a lokacin baya idan jarumi ya yi laifi muna hukunta shi.
Sabanin yanzu yarinya ma idan ta ganka ita gani take kamar kai sa’anta ne, ko yaro ya zo ya ga kamar kai sa’an sa ne, don haka akwai gazawa a shugabancin yanzu ba kamar na baya ba.
A saboda haka yanzu idan yarinya ta yi abu idan za a yi mata fada wai sai a ce a sama tana da babba, wanda ni ban yarda wannan uziri ba ne, don haka abubuwa ne suka sauya har ta kai ga an samu kai a irin wannan halin.”
Dimokuradiyya ta rawaito cewa a karshe ya yi kira ga masu harkar fim da su gyara harkokin su domin saita masana’antar zuwa tsari mai dorewa, da kuma tarbiyya.
A wani labarin kuma: Gwamnatin Jihar Kogi Ta Yi Jana’izar Gawarwaki Sama Da 100
Gwamnatin Kogi ta gudanar da jana’izar gawarwaki 130 da ba a bayyana masu su ba da aka ajiye a dakin ajiye gawarwaki na gwamnatin tarayya (FMC) da ke Lokoja.
Mrs Elizabeth Arokoyo, Babban Manajan Hukumar Kula da tsaftar muhalli da shara ta jihar Kogi ta bayyana haka yayin da take tattaunawa da manema labarai a ranar Lahadin nan.