Shirin Barkwanci na gidan Talbijin da aka dade a na jira Wato Gidan Badamasi Zango na 4, zai fara karade Talbijin a Ranar 6 ga watan Janairun shekarar 2022.
Malam Falalu Dorayi Wanda shine Mai daukar dauyin Shirin ya ce, Zango na 4 Na Shirin zaifi kayatarwa feye da wadanda aka shirya a baya, Saboda an Sami Karin kwararrun jaruman Barkwanci da suka taka rawa a Shirin fiye da na da.
Falalu ya Kuma bayyana cewa, an dauki Shirin Fim din ne a wurare daban daban dake fadin jihar Kaduna, yayin da kuma aka Sanya wasu kayatattun sashi sashi a Fim din, domin Karawa Shirin armashi.
Kazalika ya ce, Shirin na Gidan Badamasi na daya daga cikin Shirye-Shiryen Fina-Finan Hausa da suka fi Karbuwa a wurin Masu Kallo , kamar yadda dama aka shirya shirin domin Al’uma.
KARANTA WANNAN LABARIN:Mutane Hudu Ne Suka Mutu, Yayin Da Fusatattun Matasa Suka Kone Motocin Biyu A Birnin Shehu
“Gidan Badamasi Zango na 4 zai kasance jerin shirye-shirye masu ban sha’awa, tun daga farko, Saboda mun amince da karbar bayanan masu kallo kuma hakan ya sanya shirin ya zama abun Soyuwar Al’uma,” in ji shi.
Zango na 4 na Shirin ya Sami Manyan Jarumai Maza da Mata da suka Hadar da Hadiza Gabon, Adam A Zango, Nabiruska, Bosho, Dan Kwambo, Falalu A Dorayi, da dai sauran su.