Masarautar bade a jahar Yobe, ta roki sanata Ali Ndume, da Danjuma goje, kan su janye su marawa sanata Ahmad Lawal shugaban masu rinjaye a matsayin shugaban majalisa ta tara.
Manyan masu Mukamai a masarautar ne suka yi wannan kira. Alhaji Mamman Suleiman, da Alhaji Muhammad Gagiyo, Wanda sune sukayi magana a madadin masarautar a Yau asabar din nan, sun ce Mara masa baya yazo dai dai da muradin arewa maso gabas da Najeriya, Baki daya, inji su.
Suleiman yace matsayin sanatocin biyu masu kishin yankin Arewa, a na sa ran zasu bashi goyon baya duba da yadda jam’iyyar (APC) ta amince mishi.
Yace Najeriya a shekaru hudu da suka gabata ta wahala kan rigingimun siyasa tsakanin majalisa da Gwamnatin tarayya Wanda ba’a fatan hakan ya sake afkuwa.