Mai Martaba Sarkin Bauchi Dakta Rilwanu Suleiman Adamu ya dakatar da Alhaji Shehu Abdullahi daga sarautarsa ta Wakilin Birnin, sakamakon abinda aka bayyana da raina magabata.
Wakilin Birni Wanda Dan Majalisa ne dake wakiltar Wajen Garin Bauchi a majalisar wakilan tarayya, ya tafi majalisar ce karkashin inuwar Jam’iyyar NNPP Mai alamar Kwando da kayan marmari a zaben gama gari da ya gudana a shekarar 2019.
Cikin wata sanarwa da majalisar Masarautar ta fitar mai dauke da sanya hannun Nasiru Musa Maidala a madadin Sakataren Masarautar, ta ce matakin tube wakilin Birnin ya biyo bayan wata ganawar gaggawa ne da ta yi a yau Lahadi.
Ta kara da cewa sau dama an sha gargadinsa bisa irin halin rashin ɗa’a da kuma raini da yake nuna wa masarautar wanda ba al’adar masarauci ba ne hakan amma ya yi kunnen uwar shegu.
Kadan daga cikin halin rashin ɗa’a ta ce ya yi akwai sanya alkyabba da kandiri kana ya shiga kan sarki gaba gadi ba tare da shamaki, kuma hakan ya saɓa wa dokar masarauta.
Har wa yau ta ce halin da Wakilin Birni ya nuna a fadar gwamnatin Jihar Bauchi yayin ziyarar Gaisuwar ga Gwamnan Jihar Sanata Bala Muhammad na daga cikin al’amarin da ya janyo taron da ya tube maka rawani.
Ko da yake da ma jama’a da dama sun yi hasashen irin yadsa wannan Sallar za ta kasance sa wakilin na birni, kasancewar shi ma’abocin hawa dawaki.
Kawo yanzu da muke haɗa muku wannan rahoto dai ba nu samu ji daga bakin Dan majalisar ba, amma za mu ci gaba da bibiyar lamarin don kawo muku bayanai.