Majalisar Masarautar Bauchi ta yi Allah-wadai da harin da aka kaiwa sarakunan Bauchi Alhaji Rilwanu suleimanu Adamu da na Dass Alhaji Usman Bilyaminu Usman a hanyarsu ta zuwa Bogoro domin halartar bikin tunawa da marigayi Baba Gonto na shekara 21 a Tafawa Balewa.
Masarautar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Galadiman Bauchi, Sa’idu Ibrahim Jahun ya karanta a karshen taron majalisar a Bauchi a jiya.
Sanarwar ta samu sa hannun babban Shugaban Kungiyar kansilolin Bauchi, Alhaji Bala Abubakar Attahiru Ajiyan, da sakataren, Alhaji Shehu Mudi Mohammed.
Masarautar ta ce an farfasa motocin da ke cikin ayarin motocin da suka hada da na sarkin Dass da Bauchi, lamarin da ya tilasta wa sarakunan komawa baya don gudun asarar rayuka da dukiyoyi.
Ta bayyana lamarin a matsayin na dabbanci, tsokana, da kuma yaudara, sannan ta bukaci gwamnatin jihar da ta tarayya da su kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika tare da gurfanar da su a gaban kuliya domin ya zama izina ga masu kokarin yin hakan a gaba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa bikin tunawa da marigayi Baba Gonto karo na 21 ya rikide zuwa tashin hankali yayin da wasu fusatattun matasa suka yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da taron tare da farfasa wasu motoci, da kuma kona gidaje 10 da wurin taron.