Majalisar Masarautar Bauchi dake arewa maso gabashin Najeriya ta yi amai ta lashe dangane da hukuncin da ta yanke cewa babu maganar hawan Sallah a bana sakamakon barazanar matsalar tsaro a Jihar.
A Jiya ne masarautar ta fitar da sanarwar haramcin hawan Sallar da aka saba kowace shekara, inda ta ce hakimai da dagatai ne kawai za su hallara don hawan Sallah amma su din ma ba tare da dawakai ba.
Cikin wata sanarwa da Sakataren Masarautar Nasir Musa Maidala ya fitar, ya ce masarautar ta dauki wannan mataki ne a wani taron gaggawa da ta gudanar a jiya Lahadi dangane da bukukuwan Sallar dake tafe, to sai dai a yanzu haka ta ce ta sauya shawara.
Har ila yau sanarwar ta kara da cewa gaishe-gaishe da masu rawani suka saba yi musamman izuwa gidan Gwamnati don mika mubaya’a wa Gwamnan Jiha bisa al’ada, tana nan daram a dawakai, ba kamar yadda aka ce a mota ce za a je ba wannan karo.
Nasir Mu’azu wani Makusancin fadar Bauchin ya tabbatar wa wakilin Mu a Bauchi sahihancin wannan labari
Daga bisani Sanarwar ta bukaci al’ummar musulmi da kowa ya bi doka don a zauna lafiya, domin an ce zama lafiya ya fi zama ɗan sarki.