• An kaddamar da kwamitin zai kula da auran Dan Shugaba kasa Muhammadu Buhari wato Yusuf Buhari.
• A nasaran cewa Yusuf zai angwance da Sarauniya Zahra ce daga Masarautar Bichi na jihar Kano.
• Yusuf Buhari da Sarauniya Zahra sun hadu ne da junan su a Masarautar Kasar England lokacin bikin kammala karatun su.
Yusuf da ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala shirye-shirye angwance wa da yarinyar Mai Martaba Sarkin Bichi, Saraudiya Zahra Ado-Bayero a ranar 20 ga watan Ogustan shekaran 2021.
Mai Magana da yawun Masarautar Bichi Lurwanu Malikawa ne, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Asabar, inda ya ce, Sarkin Bichi Alhaji Nasir Ado-Bayero ya kaddamar da kwamitin Mutum 145 da zasu shirya dauren auren.
A cewar sanarwar kwamitin shi ne zai kuma shirya bikin amsan sandan Girma na Sarkin, Wanda Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje zai bada.
Kazalika sanarwar ta ce, Hakimi garin Bagwai Nura Ahmad wato Madakin Bichi, shi ne zai iya kasance wa jagoran kwamitin, da kuma Abba Waziri wato Falakin Bichi a matsayin sakatare.
KARANTA WANNAN LABARIN: Manoman Rani dake Jigawa Sun Sami tallafin aikin Naira Billiyan 10
Lokacin da ya ke kaddamar Kwamitin, Sarkin Bichi wanda Madakin Bichi ya wakilce shi, ya ja hankalin mabobin kwamitin da su jajirce matuka, domin cimma nasaran wannan gagarumin daurin auren.
Bugu da kari sanarwar ta ce, daurin auren ka iya gudana a ranar 20 ga watan Ogustan shekarar nan, ya yin da bikin amsan sandan girman zai gudana a ranar 21 gawatan gobe, a fadar Masarautar ta Bichi.
Yusuf Buhari sun hadu da sarauniya Zahra ce a Kasar England, inda a nan ne dukkannin s,u su ka yi bikin kammala karatun su.