…Mai martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, ya kaddamar da sabuwar tashar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a kauyen Yal’lami da ke karamar hukumar Bichi ta jihar Kano.
Mai martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero ya kaddamar da sabuwar tashar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a kauyen Yal’lami dake karamar hukumar Bichi ta jihar Kano wanda masarautar ta bayar tare da hadin gwiwar wani kamfani mai suna Sand Stream Nigeria Limited.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Yayin da yake kaddamar da tashar, Sarkin ya ce, “aikin wani bangare ne na kokarin da Masarautar ke yi na samar da yanayi mai kyau ga al’ummar yankin da kuma makwabta”.
KU KARANTA KUMA Sarkin Bichi Ya Shirya Taron Addu’ar Neman Zaman Lafiya
Sarkin na Bichi ya ce “Fatanmu shi ne sabuwar tashar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana za ta taimaka wajen bunkasa kananan masana’antu da inganta harkokin zamantakewar al’ummar yankin.”
Yayin da ya bukaci jama’a da su yi amfani da wannan damar ta hanyar da ta dace, Sarkin ya kuma tabbatar da cewa masarautar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen samar da wutar lantarki, yana mai ba da tabbacin cewa za a kuma kara kaimi a fannonin ilimi, lafiya, noma da kasuwanci don baiwa al’ummar Masarautar damar samun damar yin amfani da wutar lantarki domin dogaro da kai.
Tun da farko, Shugaban Kamfanin Sand Stream Nigeria Limited, Alhaji Ibrahim Abba Gana, yayin da ya bukaci jama’a da su kula da shirin, ya ce sama da gidaje 350,000 ne ake sa ran za su ci gajiyar shirin.
Da yake mayar da martani a madadin al’ummar Yal’lami, Alhaji Hashim Sale Yal’lami ya yaba wa sarkin bisa zabar al’ummar da za su gudanar da aikin tare da ba da tabbacin za su yi amfani da wannan damar wajen bunkasa harkokinsu na zamantakewa da tattalin arziki. Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
A Wani Labarin Kuma An Haramta Duk Wata Nau’in Zanga-zanga A Jihar Nasarawa — Yan Sanda
Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa tana mai sanar da jama’a cewa an haramta duk wata zanga-zanga a fadin jihar.
Don haka ta ce an haramta duk wata zanga-zangar da aka shirya gabatarwa a ƙarƙashin kowane irin tsari.