By Abbas Yakubu Yaura
Masarautar Gaya tace zata hada hannu da jami’an kula da ababen hawa na jihar kano wajen kawo karshen yawaitar haduran dake afkuwa a manyan hanyoyin dake ƙarƙashin masarautar.
DUBA WANNAN LABARIN: Har Yanzu Buhari Bai Isa Filin Taro Na APC Ba, Wakilai Suna Jiran Kada Kuri’ar Zabe
Maimartaba Sarkin Gaya Dakta Aliyu Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin daya karbi bakunchin kwamandan shiyyar Wudil na masu kula zirga-zirgar Ababen hawa Daniel Danjuma Auta a fadarsa.
Aliyu Ibrahim yace majalisar masarautar zata umarci dukkan hakimanta dasu fadakar da al’ummar su muhimmancin yin tuki cikin natsuwa da hana su gudun wuce sa a.
Yakuma basu tabbacin zai sa baki wajen ganin an basu aron gidan hukumar sadarwa ta NITEL domin su sami matsiguni a garin yakuma ce kwanan nan Gwamnatin jihar Kano zata samar da gidaje dari shida a masarautar don amfanin yan asalin yankin.
Dayake jawabi kwamandan shiyyar na Wudil Daniel Danjuma Aura yace sun zo fadar ne don neman gudunmawar maimartaba Sarkin wajen ganin sun gabatar da matsalolin dake addabar shiyyar kamar rashin wadatattun kayan aiki da matsuguni ga ma’aikatan shiyyar.
Danuel auta yaja hankalin direbobi dasu guji dora kaya da yawa akan mota yana haifar da afkuwar hatsari da gudun wuce sa’a yakuma yi godiya ga Maimartaba Sarkin bisa yaba musu saboda gudunmawar dasuka taka alokacin bukin baiwa sarki sandar girma.