Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace katin Dan kasa yana da muhimmanci a wajen al’ummar kasar nan duba da yadda al’umma suke yawan tafiye tafiye zuwa kasashen waje.
Mai martaba sarkin ya bayyana haka ne lokacin da Shugaban Hukumar samar da Katin Dan Kasa wato National Identity Management Agency (NIMA) suka kai masa ziyara a fadarsa.
Mai Martaba Sarkin wanda Madakin Kano ya wakilta yace Masarautar Kano zata mara musu baya wajen fadakar da dagatai da masu unguwanni don sanin mahimmanci katin Dan kasa.
KARANTA ANAN: An Rantsar Da Sabon Shugaban Ƙasar Kenya, Bayan Nasara A Zaben Kasar
A nasa jawabin shugaban Hukumar samar da Katin Dan Kasan Alhaji Abdullahi Ahmed yace sun je fadar Sarkin Kano ne don neman goyon bayan masarauta don samun nasarar gudanar da aiyukansu don jama’a su fahimcin muhinmancin Katin Dan kasa.
Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya rawaito cewa masarautar ta kano zata basu hadin kai da goyon baya wajen fadakar da al’umma kan mahimmaci katin Dan kasa yake dashi.
A lokacin ziyarar dai Shugaban Hukumar kula da katin shaidar Dan kasa Alhaji Abdullahi Ahmed yana tareda Daraktoci da sauran manyan ma’aikatan Hukumar.
A wani labarin kuma: An Gano Wasu Gwamnonin PDP 4 Da Yiwa Tinubu Aiki
Wani bincike ya gano wasu Gwamnoni hudu da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP dake kokarin ganin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu yayi nasara a zaben 2023.
Idan dai ba a manta ba, gabanin babban taron kasa na ranar 28 ga watan Mayu, shugabannin jam’iyyar PDP sun yi watsi da zaben shugaban kasa ta hanyar jefa kuri’a a fili, duk kuwa da cewa babbar jam’iyyar adawa a kundin tsarin mulkinta ta ce za a yi zaben shugaban kasa tsakanin Arewa.