By Abbas Yakubu Yaura
Wazirin Dansadau, Alhaji Mustapha Umar, yace sannu a hankali zaman lafiya yana dawowa a Masarautar Dansadau bayan da aka kulla yarjejeniyar zaman lafiya da sarkin ta’addanci, Ali Kachalla.
A ‘yan kwanakin nan, al’ummomin masarautar Dansadau sun fuskanci yawaitar hare-hare da kuma garkuwa da mutane daga bangaren Kachalla da wani Damina da aka kashe kwanan nan a fadan ’yan daba.
Umar yace, Kachalla ya amince da a daina tashin hankali a tsakanin al’ummomin, wanda a karshe hakan ya share fagen girbin amfanin gonakin da suke noma, sannan matafiya su bi hanyar Gusau-Magami-Dansadau mai ban tsoro wadda mutane basa iya binta.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Umar yace “Mun kuma gargadi jama’ar mu dasu guji duk wani abu da zai iya kawo cikas ga shirin zaman lafiya.Mun sha wahala sosai a matsayinmu na mutane. Muna kira ga dukkan matasa dasu baiwa zaman lafiya dama domin dorewar tsarin don amfanin kowa da kowa,” inji shi.
Umar ya bayyana cewa sun sanar da gwamnatin jihar yadda lamarin ya gudana tare da yin kira ga hukumomi dasu shirya rangadin zuwa masarautun domin ganin al’amura da kansu da kuma tsara yadda za a samar da ababen more rayuwa ga al’umma.
Sannan ya caccaki mutanen dake ikirarin cewa su ’yan yankin Dansadau ne amma suna boye a Kaduna da Abuja suna shaida wa jama’a halin da ake ciki a masarautar, inda yace, “A gaskiya ba su san komai ba a game da lamarin.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida DIG Ibrahim Mamman Tsafe (mai ritaya) ya tabbatar da cewa zaman lafiya na kara dawowa a Dansadau, ya kara da cewa babu wani danyen aiki da ‘yan fashin suka aikata a kan tudu.sannan ya ce gwamnatin jihar na daukar matakai domin magance kalubalen, inda yace matakan da hukumomi suka dauka a jihar suna biya ne saboda an ingiza masu aikata laifuka zuwa gagarabadau.