Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, ya cika alƙawarin da ya taba dauka na samar da aikin yi ga Ɗalibanda suka kammala Jami’ar Umaru Musa Ya’adua da sakamako mafi daraja wato Fist Class.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata takardar Manema Labarai mai ɗauke da sa Hannun Babban Sakatare a Ofishin Shugaban Ma’aikata na jiha, Alhaji Usman Isyaku.
Gwamna Masari ya taba shan alwashin samar da aiki ga duk dalibai yan asalin Jihar da suka Kammala Jami’ar ta UMY da sakamakon First Class.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Lagos ta hana sanya Lasifiku a Tashar Motoci
Sanarwar tace, Gwamnan yayi alkawarin hakan ne a lokacin bikin yayen Ɗaliban Jami’ar inda Gwamna Aminu Bello yayi alƙawarin samarwa Ɗaliban su 32 aiki da suka kammala Jami’ar da mataki mafi daraja wato Fist Class a Ma’aikatun Jihar.
Kamar yadda Sanarwar ta bayyana, yanzu haka daga cikin Ɗaliban waɗanda suka kammala bautar Ƙasa sun fara aiki a Jihar.
Bugu da Kari, sanarwar tayi kira ga Ɗaliban da suka samu wannan damar da su tuntuɓi Ofishin Shugaban Ma’aikata na Jihar Katsina domin samun cikakken bayanin kama aiki kamar yadda Gwamnan yayi alwashin hakan.
Comments 1