A wata sanarwa da ofishin watsa labarai na gidan gwamnatin Katsina, wanda Hassan Muhammad Tukur ya fitar ya bayyana cewa gwamna Aminu Bello Masari ya bai wa jami’an ‘yan sanda damar kama duk wani wanda aka kama yana yada labaran karya ta hanyar kafafen sada zumunta dangane da rashin tsaron jihar. Inda Masari ya ce ko da kuwa mabiya gwamnatin ne aka kama su da wannan laifin, a yi maza a cafke su.
Alhaji Aminu Bello Masari ya yi wannan bayanin ne a yayin da Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sandan jihar,AIG Sadiq Abubakar Bello ya kai masa ziyara a gidan gwamnati dake Katsina.
Gwamnan har wala yau ya ce gwamnati ta ji dadin yadda jami’an ‘yan sanda suka rika magance matsalar tsaron jihar a baya. Inda ya nemi da ‘yan sanda da su jajirce wajen magance matsalar ‘yan bindiga a jihar.
Ya tabbatar musu da cewa gwamnati za ta ci gaba da ba su tallafi da gudummawa wajen ganin sun gudanar da ayyukansu.