Gwamnatin Jihar Katsina ta rarraba filaye ga mutane 728 da filayen su suka shiga aikin fadada Filin Jirgi na Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina.
Haka zalika Gwamnatin ta bayar da filayen ga mutane 216 da aikin Sabuwar hanyar Masanawa-Sullubawa-Kofar Guga ya shafa a cikin Birnin Katsina.
Masu filayen da aikin fadada Filin Jirgin ya shafa sun fito ne daga kauyen Bakuru da ke Gundumar Modoji.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari yayi gargaɗin Ɗaukar Fansar kisan Fatima, yace ana bincike kan bidiyon
Rarraba filayen ga wadanda aikin ya shafa kari ne bisa ga kudaden diyya da Gwamnatin ta Masari ta basu domin farnta masu rai.
Ma’aikatar Filaye Da Safiyo ta Jihar Katsina ce ke gabatar da takardun filayen ga wadanda suka amfanan a halinda ake ciki.
Da yake gabatar da takardun filayen ga wadanda suka amfanan, Kwamishinan Ma’aikatar Alhaji Usman Nadada ya bayyana cewar, bayar da filayen ya biyo bayan yunkurin Gwamna Masari na tausaya wa ga wadanda suka amfana.
Alhaji Usman Nadada wanda Daraktan Filaye na Ma’aikatar Alhaji Mustapha Zubairu ya wakilta, ya bayyana cewar, tuni Gwamnatin ta kuma biya kudaden diyya ga wadanda ayyukan ya ritsa da su.
Kwamishinan ya nuna Jin dari akan yadda mutanen suka nuna halin da’a da goyon baya a lokacin aikin gabatar da takardun filayen a gare su.
Shima a nashi jawabin, Daraktan Harkokin Mulki na Ma’aikatar Sade Bara’u, ya tabbatar da cewar Ma’aikatar zata gudanar da gaskiya da adalci ga dukkan wadanda aikin ya shafa a lokacin gabatar masu da takardun filayen su.
A madadin wadanda suka amfana, Ummaru Karoni ya yaba wa Gwamna Aminu Masari akan wannan karamci da ya yi masu, sai ya yi addu’a akan Allah ya saka mashi da mafificin alkairi.
Shima a nashi jawabin, Wakilin Magaji Modoji Hisham Adam Shinkafi ya bayyana cewa masu rike da Sarautu zasu yi aiki tukuru wurin ganin Ma’aikatar ta samu nasarar aikin.
Comments 1