Gwamna Aminu Bello Masari ya yi ga jami’an tsaron ƙasar nan da su kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga a jihar Katsina dama wasu yankuna na arewancin ƙasar nan.
Masari ya bawa jami’an tsaron wannan umarnin da cewa kada su bar kowane ɗan bindiga a raye, dukkaninsu ya kamata su dandana ukuba kamsr yadda suka saka rayuwar mutane a cikin mawuyacin hali.
Gwamnan ya bayyana hakan a yayin da yake kai ziyarar jaje ga mazauna sansanin ‘yan gudun hijira dake Faskari, kadisau, da kuma Dandume a ranar Lahadi.
Ya ƙara da cewa, matukar ana bukatar zaman lafiya ya wanzu a arewa, to tabbas sai jami’an tsaro sun tashi tsaye wajen kawar da ayyukan ‘yan bindiga.
‘Yan gudun hijirar, ya musu alƙawarin basu kulawa da ta shafi tsaro, harkar lafiya da kuma kula da su da kayan abinci.