Direbobin babur mai ƙafa uku sun koka kan yadda har yanzu hukumar kula da zirga zirgar ababen hawa ta Kano wato KAROTA, ta gaza cika alƙawarin sanya musu na’urar ‘Tracker’ a cikin baburan nasu.
Tun a bara ne dai hukumar ta fito da tsarin sake yin rijista lambar baburan, da kuma biyan maƙudan kuɗaɗe da nufin samar musu da na’urar ‘Tracker’ ɗin wadda zata taimakawa hukumar wajen gano masu aikata laifuka a cikinsu.
Sai dai har kawo yanzu, masu baburan na ƙorafin rashin basu na’urar duk da yawan bibiya da suke yi.
Ko da aka tuntunbi jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Nabulusi Abubakar Kofar Na’isa wanda ya ce, tuni hukumar ta samar da na’urar har ma ta aike da su zuwa kowacce ƙaramar hukuma.
Har wa yau, yace kowane mai babur ɗin na Adaidaita sahu ya koma zuwa ƙaramar hukumarsa ya bibiyi tasa na’urar don ya fara amfani da ita.