Gwamnatin Legas ta ce karin mutum 49 sun warke daga cutar korona.
Sanarwar da ma’aikatar lafiya ta jihar Legas ta fitar a shafita na Twitter dake @LSMOH
ta ce wadanda suka warke cikin mutum 49 din sun hada da mata 28 da maza 21 wanda a cikinsu akwai dan asalin kasar Girka.
A cewar sanarwar ma’aikatar lafiyar yanzu haka adadin mutum 187 suka warke a jihar.