Cibiyar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya, NCDC sun bayyana cewa ya zuwa hada wannan rahoto akwai mutum 14,848 da suke dauke da cutar korona a jihar Legas.
NCDC ta bayyana hakan ne a cikin rahotonta kan cutar Korona na ranar 28 ga watan Yulin 2020.
Inda a ranar aka bayyana cewa an samu sabbin murum 212 da ke dauke da cutar a jihar cikin mutum 624 da aka samu suna dauke da cutar a jihohi 18 a ranar 28 ga Yulin.
A cewar NCDC, an yiwa mutum 72,225 gwajin cutar Korona a jihar Legas kawai ya zuwa wannan rana. NCDC ta tabbatar da cewa cikin mutum 272,748 da aka yiwa gwajin korona a fadin Nijeriya, jihar Legas ce akan gaba na wadanda aka yiwa gwajin cutar. Sai kuma birnin tarayya Abuja da mutum 29,891 sai jihar Kano, Oyo da Edo da mutum 29,762, sai 16,598 da kuma 12,133.
Rahoton ya tabbatar da cewa ma’aikatan lafiya 25 da ake lura da su sakamakon kamuwa da cutar, sun warke harma an sallame su cikin ma’aikatan lafiya 2,129 da suka kamu da cutar a jihar.
Yanzu dai jihar Legas na da mutum 14,848 cikin mutum 41,804 dake dauke da cutar a Nijeriya.
Alkaluman hukumar lafiya ta duniya, WHO ta nuna cewa mutum 873,378 ke dauke da cutar a Afrika, a yayin da mutum 520,000 suka warke, sai kuma 18,487 suka mutu.