Cibiyar dake lura da cututttuka masu yaduwa ta Nijeriya, NCDC ta bayyana cewa a ranar Talata an sake samun sabbin mutum 148 da suke dauke da cutar Korona fadin kasarnan. Lamarin da ya sanya masu cutar yanzu suka kai 2950,
NCDC sun tabbatar da cewa sabbin mutum shida sun sake mutuwa a Nijeriya, inda adadin wadanda suka rasa ransu yanzu suka kai 98.
Cibiyar ta tabbatar da hakan ne a shafinta na Twitter a daren ranar Talata.
“an samun 43 a Legas, 32 a Kano, 14 a Zamfara, 10 a FCT, 9 a Katsina, 7 a Taraba, 6 a Borno da Ogun, 5 a Oyo, 3 a Edo, Kaduna da kuma Bauchi, sai 2 a jihohin Adamawa da Gombe, sai daya-daya a Filato, Sokoto da Kebbi.” Inji NCDC