Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta cafke akalla mutane 12 da ake zargi da damfarar intanet a ranar Juma’a.
An cafke wadanda ake zargi ne, da damfarar yanar gizo a yankunan Alapata da Awotan da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Wadanda ake zargin sune: Adetola Oluwaseyi Francis; Yusuf Sadam Opeyemi; Usman Adam Abudulahi; Usman Adams Shehu; Ogunleye Timidehin Paul; Omobowa Oluwagbemileke Israel; Owoade Kehinde Elijah da kuma Kamorudeen Sodiq Akano.
Sauran sune: Adeboye Abdulazeez Ayodeji; Ojekunle Tobiloba Micheal; Adewole Peter Adewunmi da Adetola Olamilekan Abidemi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Majalissar Dattijai ta Bukaci FG ta Sanya dokar ta Baci kan Manyan hanyoyin kasar nan
Sanarwar da Kakakin Yada Labarai na hukumar, Wilson Uwujaren ya fitar ya ce, an kama da dama daga cikin wadanda ake zargi da ikirarin cewa, sun kammala karatun digiri na biyu bayan da aka gudanar da binciken sirri kan zarginsu da hannu cikin laifukan da suka shafi intanet.
Sanarwar ta kara da cewa, a lokacin da aka cafke su, an kwato jerin wasu takardu na yaudara da wasu kayan aiki da ake zargin anyi amfani da su wajen aikata laifukan.
Sanarwar ta ba da jerin abubuwan da aka samu a hannun wadan da ake Zargin kamar haka: Toyota Corolla, wayoyin zamani da kwamfyutocin tafi -da -gidanka, inda ta kara da cewa “za a gurfanar da su a gaban Kotu, da zaran an kammala bincike.”