Masu Zaben Sarki a masarautar Kano da ke Najeriya sun shigar da karar Gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje a gaban kotu, inda suke kalubalantar matakinsa na kirkirar sabbin masarautu hudu a jihar.
Masu Zaben Sarkin da suka hada da Sarkin Dawaki, Maituta Alhaji Bello Abubakar da Sarkin Bai, Alhaji Mukhtar Adnan da Madakin Kano, Alhaji Yusuf Nabahani da Makaman Kano, Alhaji Sarki Ibrahim Makama na kalubalantar Ganduje a gaban babbar kotun jihar.
Har ila yau, Masu Zaben Sarkin , sun shigar karar shugaban Majalisar Dokokin jihar, Kabiru Alhassan Rurum da ita kanta gwamnatin jihar da kuma sabbin sarakunan Gaya da Rano da Bichi da Karaye da Gandujen ya nada.
Ana saran wadanda ake zargin su bayyana a gaban kotun cikin kwanaki 21 da samun takardar kira daga kotun.
Masu Zaben Sarkin sun ce, dokar kirkirar sabbin masarautun ta yi hannun riga da tarihin masarautar Kano.
Gabanin wannan lokaci dai, wata kotu da ke zama a Ugogo ta umarci Gwamnan jihar da ya dakatar da shirinsa na mika takardun nadi da sandar girma ga sabbin sarakunan na Gaya da Rano da Bichi da kuma Karaye.