‘Yan ta’adda na neman a biya su N100m kudin fansa kan kowane fasinja, daga cikin fasinjoji 43 da aka sace a Kaduna, wadanda har yanzu suke hannunsu, inji rahoton jaridar The PUNCH.
An sanar da bukatar ga iyalan wadanda aka yi garkuwa da su a makon jiya.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyar bayan da wasu da dama dauke da makamai suka kubutar da wadanda ake zargin sun kitsa garkuwa da su daga gidan yarin Kuje da ke Abuja.
Kungiyar IS da ke yammacin Afirka ta dauki alhakin kai harin a wani faifan bidiyo da ta fitar bayan sa’o’i 24.
A yayin harin, sama da mayakan Boko Haram 300, wadanda aka yanke wa hukunci da sauran fursunoni, ‘yan ta’addan ne suka arce.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta sanya bayanan kwamandojin Boko Haram 64 a cikin ma’adanar bayanai ta Interpol da suka tsere daga hannunsu a lokacin harin.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewa ‘yan ta’addan sun kai hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, inda suka kashe takwas tare da yin garkuwa da fasinjoji akalla 61.
A wani bangare na bukatunsu, sun bukaci a sako kwamandojin ‘yan ta’adda 15, da ‘ya’yansu da sojoji ke tsare da su da kuma wasu makudan kudade da ba a bayyana adadinsu ba.
A ranar 12 ga watan Yuni ne ‘yan ta’addar suka sako wasu mutane 11 da aka yi garkuwa da su bayan shafe kwanaki 75 a hannunsu, yayin da wasu bakwai suka sake samun ‘yancinsu a ranar Asabar.
Rahotanni sun ce an sako wadanda lamarin ya rutsa da su ne ta hanyar taimakon mawallafin jaridar Desert Herald da ke Kaduna, Malam Tukur Mamu, wanda ke tattaunawa da mayakan.
Da yake karin haske kan lamarin a ranar Lahadi, wani dan uwan wadanda aka sace, wanda bai so a buga sunansa ba, ya shaida wa daya daga cikin wakilanmu cewa, ‘yan ta’addan na neman kowane iyali Naira miliyan 100 na kudin fansa domin a sako ‘yan uwansu.