Mai rahoton jaridar PUNCH, Okechukwu Nnodim, wanda aka sace a ranar 3 ga watan Fabarairun shekararnan tare da wadansu mutumin biyu a gidansu dake Kubwa a birnin tarayya Abuja, an sake su kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Matar Nnodim, Oluchi Nnodim, ita ce ta tabbatar da labarin sakin na su a ranar Lahadi, inda ta ce an saki mijinta ne a tsakiyar daren ranar Asabar.
Ta ci gaba da cewa; ba mijinta kadai aka saki ba, an sake shi ne tare da wadansu yara guda biyu da aka sace su tare.
“na ji dadi an same shi a raye. Na godewa Allah bisa abin da ya yi min. Bai yadda makiya sun yi mana dariya ba”, inji matar ta shi.
A karshe ta godewa kowa da kowa bisa gudummawar da suka bayar wajen ganin mijin na ta an sake shi, inda ta yi addu’ar Allah ya biya su.
Nnodim tare da mutum biyun sun kwashe kwanaki uku a hannun masu garkuwa da jama’ar, wanda suka ce su a gidansu bayan da suka bude wuta a yayin shiga gidan.
Masu garkuwar dai sun nemi da a biya naira miliyan 10 kafin su sake su, sai dai bayanai ba su tabbatar da ko an biya kudin ba kafin su sake su.