Rahotanni sun bayyana cewa masu garkuwa da kwamishinan yada labarai, al’adu da yawon bude ido na jihar Nasarawa, Lawal Yakubu sun rage kudin fansa daga abunda suka nema don sakinsa zuwa Naira miliyan 20.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, an yi garkuwa da Lawal ne a gidansa da ke Nasarawa Eggon, shedikwatar karamar hukumar Nasarawa Eggon ta jihar a ranar Litinin.
Yan Sanda Sun Kama Yan Mata Da Maza Kan Zargin Ɗaukar Hoton Tsiraicin Mutane
Kwanaki biyu kafin a yi garkuwa da kwamishinan, ma’aikacin Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati (GSSS), da ke karamar hukumar Nasarawa Eggon, Auta Nasela, wasu ‘yan bindiga ne suka kashe shi a gidan ma’aikata yayin da wani ma’aikacin ya samu raunuka.
Daily trust ta tattaro cewa an tura dakaru hudu na musamman daga Barikin Doma, shedikwatar karamar hukumar Doma ta jihar a Nasarawa Eggon.
Wani dan uwa da ya nemi a sakaye sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa, wadanda suka yi garkuwa da su sun tuntubi iyalan da misalin karfe 10:30 na safiyar ranar Alhamis inda suka bukaci a biya su Naira miliyan 20.
Sai dai ya bayyana cewa iyalan sun yi tayin biyan masu garkuwa da mutanen Naira miliyan 4.5, amma masu garkuwar sun ki amincewa da wannan tayin tare da kashe layin wayarsu a fusace.
Ya ce, “Masu garkuwan sun kira ‘yan uwa daidai karfe 10:30 na safiyar ranar Alhamis din nan inda suka rage kudin fansa daga Naira miliyan 100 zuwa miliyan 20.”
A kwanakin baya ne gwamnan jihar Abdullahi Sule ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da na sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a fadin kananan hukumomi 13 na jihar sakamakon bayanan sirri da hukumomin tsaro suka samu a jihar.
Hakazalika, hukumar wayar da kan jama’a ta kasa ta yi gargadin cewa ‘yan bindiga na daukar yara aikin soja a jihar Nasarawa.
Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan DSP Rahman Nansel, ya ce hadin gwiwar rundunar ‘yan sanda ta wayar tafi da gidanka, sashin yaki da masu garkuwa da mutane, jami’an soji, ‘yan banga, har da mafarautan yankin sun zagaye yankin domin kubutar da kwamishinan da aka sace.