Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Najeriya (NULGE) a ranar Talata ta bukaci a gaggauta sakin mambobinta 12 da ke aiki da karamar hukumar Zariya da aka yi garkuwa da su a ranar 8 ga watan Nuwamban shekarar 2021.
Kungiyar wadda ta koka da shirun da gwamnatin jihar Kaduna ta yi tun bayan sace su, ta ce wadanda suka yi Garkuwa da mambobin nata, sun nemi a biya su Naira miliyan 40 a matsayin kudin fansa.
Shugaban kungiyar ta NULGE na kasa, Kwamared Akeem Ambali Olatunji, wanda shine ya yi wa manema labarai karin haske a ranar Talata a Abuja, ya yi gargadin cewa kungiyar ba ta da wani zabi illa ta dauki tsatsauran mataki a fadin kasar idan har rokon da ta yi na a sako ma’aikatan ta shiga kunnen uwar shegu.
A cewar shugaban NULGE, tara daga cikin ma’aikatan 12 mata ne masu shayarwa da kuma mata masu aure, inda ya jaddada cewa dole ne a dauki matakin gaggawa don ganin an sako su ba tare da bata lokaci ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Fashewar Iskar Gas A Legas ya Kashe Mutane biyar ~ Hukumar SEMA
Ya ce an saki daya daga cikin 12 Wanda ya kasance direban motar da suke ciki ne, don ya kai rahoto ga iyalan wadanda aka sace.
“Wadannan ma’aikatan sun kasance a hannun masu garkuwa da mutane tun ranar 8 ga watan Nuwamba 2021 wanda hakan ya haifar da wahalhalu a zukatan dangi da shugabannin kungiyar.”
“Abin ya dame mu saboda gwamnatin jihar Kaduna ta yi shiru har ya zuwa yanzu kamar dai komai ya lafa, lokacin da ya zama hadari ga ma’aikata su je aiki a cikin sa’o’in aiki ko kuma su yi tafiya cikin karamar hukuma ko jiha; Ina kira da babban murya”
Comments 1