Wanda ya rasu, masu garkuwa da mutane sun sace shi a Ƙaramar Hukumar Eleme ta Jahar Rivers a watan Satumba, tare da kashe shi, amma sun buƙaci iyalan shi su biya Naira miliyan 200 a matsayin kuɗin fansa.
Inda daga bisani aka kai rahoton ga Ƴan sanda, wanda hakan ya bada nasarar kama guda 3 daga cikin wanda ake zargin sun kashe shi.
Dayake jawabi ga Manema Labaru a wurin da aka gano gawar Babban Sojan mai ritaya ɗan shekaru 64, Kwamishinan Ƴan sandan Jahar Rivers CP Eboka, yace lamarin ya faru ne a ranar 18 ga watan Satumba na Shekarar 2021, amma ba’a sanar da ƴan sanda ba, sai bayan wata ɗaya da sace shi.

KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan Kasar Libiya Na Karbar Katunan Zabe Gabanin Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa
Eboka yace daga lokacin da aka sanar da ƴan sanda, sun fara gudanar da bincike ta hanyar sirri, tare da kama uku daga cikin wanda ake zargi, da suka haɗa da Frank Ishie, Iwuji Reginald, da Gomba Okparaji.
Ya bayyana cewar wanda ake zargin sun buƙaci iyalan shi su biya kuɗin fansa, kafin su kashe shi.
Ɗaya daga cikin wanda ake zargin Ishie wanda yayi jawabi ga Manema Labaru, ya tabbatar da aikata laifin da ake zargin su da aikatawa.
Wanda ake zargin yace sun sace shi a Agbonchia ta Ƙaramar Hukumar Eleme, amma sun harbe shi a ƙafa, sakamakon ya kasance mai ƙorafi a dai-dai lokacin da zasu kaishi maɓoyar su.