By Abbas Yakubu Yaura
Basaraken gargajiya na jihar Ekiti, Emmanuel Obafemi, da wasu ‘yan kasuwar sayar da koko guda biyu da aka yi garkuwa dasu a Ijan Ekiti dake karamar hukumar Gbonyin ta jihar Ekiti a makon jiya sun shaki iskar ‘yanci.
Yayin da aka dauke basaraken daga gonarsa dake kan titin Ijan zuwa Ado a ranar Alhamis din data gabata, inda aka yiwa masu sayar da kokon kwanton bauna a daji dake kan titin Ijan-Ise ranar Kirsimeti.
Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa wadanda lamarin ya rutsa dasu sun sake samun ‘yancinsu da sanyin safiyar ranar Laraba bayan da iyalan su suka biya kudin fansa ga mutane da ake tsare dasu kimanin naira miliyan 2m kowannen su.
Wata majiyar mai tushe data shaida wa manema labarai a Ado Ekiti cewa iyalan Obafemi sun biya naira miliyan 2m kafin a sallame shi, yayin da sauran ’yan kasuwar koko biyu suka biya Naira miliyan 2m, wanda jimillar kudin ya kai naira 4m kafin a sake su su tafi da misalin karfe 3 na safiyar ranar (Laraba).”
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Sunday Abutu, ya tabbatar da sakin mutanen, inda ya kara da cewa tuni suka koma cikin iyalansu.
Abutu ya bayyana cewa, “an sako (wadanda lamarin ya rutsa dasu) da misalin karfe 3 na safiyar ranar Laraba. Yanzu suna tare da iyalansu, cikin koshin lafiya. Sai dai sakin basaraken ya biyo bayan aiki tukuru da jami’an hadin gwiwar ‘yan sanda da Amotekun da mafarauta suka yi a dajin domin neman wadanda aka sace.
“Muna tabbatar wa mazauna jihar Ekiti tsaro a ko da yaushe kuma muna rokonsu dasu rika ba mu bayanai masu amfani da za su taimaka wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasar.”