By Abbas Yakubu Yaura
Wadanda suka yi garkuwa da wani tsohon dan takarar gwamna a jihar Filato, Kemi Nshe, sun ki sakinsa fiye da mako guda da sace shi.
An tattaro cewa masu garkuwa da mutane, sun kuma yi watsi da kudi naira miliyan 7m a matsayin kudin fansa domin baiwa Nshe wanda aka sace tare da wani malamin jami’ar jihar Filato, Monday Hassan damar samun ‘yancinsu.
Da yake bayyana hakan ga majiyar Jaridar Dimokuradiyya dake Jos a ranar Lahadin da ta gabata, wasu majiyoyi da ke da alaka da bangaren na uku na dangin sa sun ce suna tattaunawa da masu garkuwa da mutanen, “yanzu sama da mako guda kenan masu garkuwa da mutane suna tsare da shi (Nshe). Masu garkuwa da mutanen ba su kuma saki malamin da aka sace tare da shi ba. Shin za ku iya tunanin sun ki karbar naira miliyan 7m da aka ba su domin a sako wadanda aka sace? Masu garkuwa da mutanen sun ce adadin kadan ne kuma suna son kari.
“Halin da ba zan iya fahimta ba ne. Amma har yanzu masu tattaunawar suna rokonsu da su ji tausayin mutanen biyu a kubutar da su, domin za ka iya tunanin irin halin da iyalai suka shiga wajen tara kudin da aka ce sun kai naira miliyan 7m a halin da ake ciki yanzu na tattalin arzikin kasar nan.”
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa a safiyar ranar Asabar din makon jiya ne wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da Nshe, tsohon shugaban karamar hukumar Shendam daga gidansa da ke Shendam.
Nshe, jigo a jam’iyyar PDP yana tare da bakon nasa, Hassan, wanda shi ne shugaban kungiyar malaman jami’o’i reshen jami’ar Jihar Filato, a lokacin da ‘yan bindigar suka kai farmaki gidan suka tafi da su inda ba a sani ba.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Ubah Ogaba, ya ce rundunar tana yin komai domin ceto wadanda lamarin ya shafa tare da damke wadanda suka aikata laifin.